1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaddamar da shari'ar mutane 14 a Ouagadougou

Zainab Mohammed Abubakar
October 8, 2021

A ranar Litinin ake fara shari'ar tsohon shugaba Blaise Compaore na Burkina Faso da wasu mutane 13, kan zargin kisan gillar Thomas Sankara a 1987.

https://p.dw.com/p/41QYg
Burkina Faso |  Prozess Thomas Sankara | Jean-Hubert
Hoto: Katrin Gänsler/DW

Kimanin shekaru 34 kenan tun bayan da aka bindige jagoran juyin juya hali kuma tsohon shugaba n Burkina Faso Sankara a wani juyin mulkin da babban amininsa ya jagoranta, batu da ya girgiza wannan kasar ta yammacin Afirka da ke da tarihin rigingimu na siyasa.

Tuni dai ake zargin magajin Sankara, Blaise Compaore wanda ya mulki kasar ta Sahel na tsawon shekaru 27 da suka biyo bayan kisan gillar. A shekara ta 2014 ne zanga zangar adawa ta kifar da mulkin Compaore, inda ya tsere zuwa Ivory Coast, kasar da ta bashi takardar shaidar zama dan kasa.

Mai shekaru 70 da haihuwar dai ya karyata zargin da ake masa na hannu a mummuna kisan gillar da aka yi wa Thomas Sankara. A wannan Juma'ar ce dai a ta bakin lauyoyinsa, Compaore ya ce ba zai halarci zaman shari'ar ta Ouagadougou.