Faransa ta fara kwashe jama'arta a Nijar
August 2, 2023Talla
Rahotannin sun yi nuni da cewa jirgin farko dauke da 'yan kasashen Turai 260 ya sauka a birnin Paris daga birnin Niamey, yayin da Italiya ta sanar da cewa kimanin mutane 87 sun sauka a birnin Rome. Dama dai Faransa ta tura da jirage kimanin uku zuwa birnin Niamey, domin kwashe 'yan Faransa da Portugal da Beljiyam da Habasha da kuma Lebanon sakamakon kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
Tuni dai ma'aikatar tsaron Spain na shirin kwaso mutane fiye da 70 daga birnin Yammai. Kasashen Turai da dama ne dai suka bayyana shirin kwashe jama'arsu daga kasar da ke karkashin mulkin soji a yanzu.