Farar hula 14 sun halaka a Burkina Faso
January 4, 2020Rahotanni daga Burkina Faso na cewa wasu fararan hula 14 akasarinsu dalibai 'yan makarantar sakandare sun halaka bayan da motarsu ta hau kan wata nakiya da aka dana a kan hanyar garuruwan Toerie da Tougan na jihar Sourou da ke arewacin kasar kusa da iyaka da kasar Mali.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito wata majiyar tsaro a yankin na cewa da misalin karfe tara na safiyar wannan Asabar ce, motar safa, dauke da fasinjoji akasarinsu dalibai da ke dawowa daga hutun Kirsimeti ta hau nakiyar da ta tashi da ita inda ko baya ga mutuwa wasu mutane 14 sun ji raunika a cikin hadarin daga cikinsu hudu munana.
Wannan na zuwa ne kwanaki 11 bayan wani harin da 'yan bindigar suka kai a garin Arbinda na arewacin kasar a jajibirin bikin Kirsimeti inda mutane 35 da suka hada da mata 31 da sojoji bakwai suka halaka.