Somaliya na fuskantar fari da yunwa
May 6, 2019Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan biyu ke bukatar taimakon agaji na gaggawa na abinci, masu aiko da rahotannin sun ce dubban jama'a a kasar na barin gidajensu daga yankunan karkara domin zuwa birane saboda farin da ya afka wa kasar a kan rashin saukar damina, A makon jiya kawai mutane dubu 44 suka yi kaura daga yankunan karkara zuwa birane a cewar MDD.