Garambawul ga gwamnatin Japan
August 27, 2007Praministan ƙasar Japon Shinzo Abbe, yayi garambawul ga gwamnatin sa , a sakamakon mummunan kayin da ya sha a zaɓen yan maljalisun dokokin da ya a ka shirya a watan da ya gabata.
Kazalika Shinzo Abbe, ya gudanar da kwaskwarima ga hukumar zartaswa, ta jam´iyar PLD mai riƙe da ragamar mulki.
A na zargin shugabanin wannan jam´iya da zama ummal ibasar kayin da ta sha a zaɓen ranar 29 ga watan juli da ya wuce.
A sakamakon wannan garambawul, ministan harakokin waje, Taro Aso ya yi murabus inda ya zama saban sakatare Janar na Jam` iyar PLD.
Ya ce ya yanke wannan shawara, da zumar farfaɗo da martabar jam´iyar wacce a halin yanzu, ruwa ya doki babban zakara.
An naɗa Nobutaka Machimura, a matsayin saban ministan harakokin waje.
Shinzo Abbe da ke shan suka daga jama´ar bayan zaɓen, ya yi tsayuwar gwamen jaki, akan kiran da ake masa, na yayi murabus daga muƙamin sa.