Gasar cin kofin Turai: 'Yan kwallo da ke da tushe da Afirka
Daga cikin kasashen Turai 24, gomman 'yan wasan da ke da tushe da Afirka, na cikin wadanda za su fafata a gasar da ke gudana daga 11 ga watan Yuni zuwa 11 ga Yuli.
Kylian Mbappe (Faransa)
Mahaifinshi dan Kamaru ne, mahaifiyarsa kuwa daga Aljeriya. Kylian Mbappe na da tushen Afirka. Yana dan shekaru 19 lokacin da kungiyarsa ta Faransa ta lashe gasar cin kofin duniya a 2018 a Rasha. Yana daya daga cikin 'yan Afirka da ke yi wa Faransa wasa, ciki har da Paul Pogba (Gini), N'Golo Kante da Moussa Sissoko (Mali), Ousmane Dembele (Cote d'Ivoire).
Romelu Lukaku (Beljiyam)
An haifi iyayen fitaccen mai zura kwallo a raga na Beljiyam a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Lukaku ya taimaka wa kungiyarsa zama na uku a gasar cin kofin duniya na 2018. Akwai wasu 'yan wasan kasar da ke da tushe daga Afirka, kamar Michy Batshuayi da Christian Benteke (Kwango) da Jeremy Doku (Ghana).
Antonio Rüdiger (Jamus)
"Iyalina sun fito daga Afirka," a cewar mai tsaron baya na Jamus, wanda iyayensa suka tsere wa yakin basasar Saliyo zuwa Berlin. Saura 'yan wasa kamar Leroy Sane da Serge Gnabry da Jamal Musiala na da tushe da Afirka. Mahaifin Musiala dan Najeriya ne, kana mahaifin Sane, tsohon dan wasan Bundesliga Souleymane Sane, ya fito daga Senegal, shi kuma mahaifin Gnabry dan kasar Cote d'Ivoire.
David Alaba (Ostriya)
Da Alaba zai yi wa Najeriya wasa, inda nan ne asalin mahaifinsa. Amma mai tsaron bayan da ke barin Bayern bayan shekaru 13, ya zabi yi wa mahaifarsa Ostriya wasa. 'Yan wasan Bundesliga kamar Valentino Lazaro (mahaifinsa dan Angola) da Karim Onisiwo (mahaifi daga Najeriya) na cikin tawagar Ostiriya a gasar cin kofin na Turai.
Breel Embolo (Switzerland)
Dan wasan gaban, haifaffen Kamaru ne. Mahaifiyarsa ta kaura zuwa Switzerland da 'ya'yanta maza guda biyu lokacin da Embolo yake shekaru shida, mahaifinsa kuwa yake Afirka. Akwai wasu 'yan wasa masu tushe daga Afirka da kasar ke alfahari da su a gasar Turan kamar Denis Zakaria (mahaifinsa daga Kwango da mahaifiya 'yar Sudan) sai Kevin Mbabu (mahaifiyarsa daga Kwango).
Memphis Depay (Netherlands)
Mahaifin Memphis Depay ya fito ne daga Ghana. Ya bar mahaifarsa zuwa Holland tun lokacin da dan wasan gaban yana yaro karami- dalili ke nan da yake son amfani da sunansa na farko kan rigunansa na wasa. Nathan Ake (mahaifinsa dan Ivory Coast) shi ma na cikin 'yan wasan Netherlands a gasar neman cin kofin Turan.
William Carvalho (Portugal)
Tuni dai dan wasan tsakiyar ya lashe kofin Turai wa Portugal a 2016, yanzu kuma haifaffen Angolan, Carvalho ya dawo neman kari. An haife shi a Luanda babban birnin Angola, sai dai tun yana yaro ya kaura zuwa Portugal. Akwai wasu 'yan wasan Portugal masu tushe daga Afirka kamar Danilo Pereira (daga Gini-Bissau).
Alexander Isak (Sweden)
Iyayen dan wasan gaba na Sweden Alexander Isak sun fito daga Eritiriya. Ya yi kwantaragin shekaru biyu a kungiyar Borussia Dortmund, amma yanzu dan wasan Real Sociedad. Mainz Robin Quaison (mahaifi daga Ghana) da Ken Sema (iyaye daga Kwango) na cikin tawagar Sweden a gasar cin kofin Turan na bana.
Glen Kamara (Finland)
Bai jima ba da dan wasan tsakiyar na Finland ya lashe gasar lig-lig na Scotland tare da kungiyar Rangers. Iyayenshi sun fito daga Saliyo, an haife shi a birnin Tampere na kasar Finland. Ya koyi sana'arsa a makarantar horar da matasa kwallo ta Arsenal.
Bukayo Saka (England)
Iyayen dan shekaru 19 da haihuwa sun yi kaura daga Najeriya zuwa Ingila. Ya samu horon iya wasa daga tawagar Najeriya, amma ya zabi yi wa Ingila wasa - sanya shi cikin gasar kofin Turai din dai, ya zo da mamaki.