Ghana: Atisayen soji don yaki da ta'addanci
June 23, 2021Samame da dakarun suka shafe kwanaki biyar suna yi ya gano maboyar wasu 'yan ta’adda. Da yake bayyana yadda al’amarin ya gudana Brigagiya janar Moses Aryee, dake shugabantar dakarun a yankin arewacin Ghana yace wajibi ne jama'a su tashi tsaye tare da bada cikakken hadin kai ga jami'an tsaro.
Ta’addanci lamari ne mai sarkakiya wanda idan ya faru kowa zai ji radadinsa domin babu wanda ya tsira. Ya tabbatarwa jama’ar Ghana cewa sojoji za su cigaba da kai samame a dajin Gbole dake yankin arewa maso yamma har sai an kakkabe 'yan ta'adda a dazuka da garuruwan Tumu da Golu.
Sai dai ko wane hali ake ciki da kuma shirye-shirye tunkarar dukkan matsalar da ka iya tasowa da kuma yanayin firgici da ake ciki, Imam Shamsuddeen Salifu, Iimamin Soja na Jihar Ashanti yayi bayani.
Yace sojoji sun yi shirin ko ta kwana muna fata jama'a za su bada hadin kai domin cimma nasarar da aka sanya a gaba.