Girgizar kasa mai karfin gaske a Japan
May 30, 2015Talla
Wata girgizar kasa da karfinta ya kai maki takwas da digo biyar a ma'aunin Richter ta afku a wani gari mai da tazarar kilimeta 800 daTokyo babban birnin kasar Japan. Ba a dai bayyana adadin mutane da wannan bala'i daga indallahi ya shafa da kuma kadarorin da suka lalace ba. Amma kuma tuni a ka rufe filin tashi da saukar jiragen sama na Tokyo. Sannan kuma harkokin sufuri na jiragen kasa da kuma motoci sun tsaya cik.
Wannan dai ita ce girgizar kasa ta biyu da ta afku a japan a cikin wannan makon da muke ciki. sai dai kuma ta farkon da ta afku a ranar Litinin da ta gabata ba ta haddasa asarar rayuka da dukiyoyi ba. Hukumomin kasar ta Japon sun bayyana cewa ya zuwa yanzu dai ba a fuskantar barazanar igiyar ruwan Tsunami.