1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwa ta hallaka mutane a Indiya

May 18, 2021

Wata guguwa mai karfin gaske hade da ruwa da iska a kauyuka da manyan garuruwa a jihar  Gujarat na kasar Indiya, ta hallaka tare tilasta sauyawa mutane da dama matsugunnai a yankin.

https://p.dw.com/p/3tX0C
Indien | Zyklon Tauktae, Mumbai
Hoto: Rajanish Kakade/AP Photo/picture alliance

Sai dai ofishin kula da yanayi a yammacin kasar ta Indiya ya ce an fara samun saukin lafawar guguwar da ta yi mummunar barna. Kimanin mutane goma sha shida ne guguwar ta hallaka wasu sama da dubu dari biyukuma aka sauya masu matsugunnai.

Hukumomin yankin na Gujarat sun bayar da sanarwar rufe tashoshin jiragen sama da na ruwa a fadin jihar.