Guguwar Eunice ta kada a Turai
February 20, 2022Talla
Guguwar wacce ke hade da ruwa da iska mai karfin gaske da ta taso daga Ireland ta ratsa kasashen Birtaniya da Faransa kafin ta zarce zuwa kasashen Denmark da Jamus. A Jamus sama da kilomita 100 na hanyoyin layin dogo sun lalace, sakamakon faduwar bishiyoyi, abin da ya gurgunta al'amuran sufuri a yankin arewacin kasar.
A yankin arewaci na Turai kuwa, an soke tashi da sauka na jiragen sama saboda iska mai karfi da ta barke. Mutane akalla biyu suka mutu a Jamus, hudu a Holland, uku a a Ingila, biyu a Beljiyam, daya a Ireland, kana wasu shida a Poland yayin da gidaje dubu 130 suka rasa wutar lantarki.