1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Belarus na shan suka kan zabe

Ramatu Garba Baba
August 10, 2020

Kasashen duniya sun soki matakin gwamnatin Belarus na musgunawa masu zanga-zangar adawa da nasarar da Shugaba Alexander Lukashenko ya yi ikirarin yi a babban zaben kasar na karshen mako.

https://p.dw.com/p/3gjXl
Weißrussland Präsidentschaftswahlen Proteste und Ausschreitungen in Minsk
Hoto: picture-alliance/dpa/V. Sharifulin

Shugabar Hukumar zartsawa ta Taayyar Turai Ursula von der Leyen ta yi kira ga gwamnatin Belarus, da ta baiyana wa al'ummar kasar ainihin sakamakon babban zaben don kawar da shakku. Daga bisani, jami'ar ta soki, matakin gwamnatin na yin amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga-zangar adawa, ta ce, musgnawa masu bore ba shi da gurbi a tsarin Turai.

Kasashe da ke membobi a kungiyar Tarayyara Turai, sun baiyana shakku a game da sahihancin zaben na Belarus, wasu daga cikinsu sun nemi a dauki matakin ladabtarwa ta hanyar sanyawa kasar takunkumi a yayin da wasu suka nemi a gudanar da taron gaggawa kan rikicin siyasar kasar.

Shugaba  Alexander Lukashenko ya gargadi masu zanga-zangar, bayan da ya ce duk wanda aka kama da laifin nuna tirjiya zai fuskanci hukunci mai tsanani, ya kwatanta masu boren da masu halin awakai 'yan amshin shatan Turai. Dubbai aka kama ake kuma ci gaba da tsarewa bayan zaben na jiya Lahadi mai cike da cece-ku-ce.