Habasha ta ƙaryata rahotannin cewa sojojinta sun kutsa cikin Somaliya.
December 11, 2006Duk da rahotannin da maneman labarai da bayanan da shaidu suka yi ta bayarwa na cewa, a jiya lahadi sun ga sojojin Habasha da ayarin motocinsu masu sulke sun ƙetare iyakarsu da Somaliya, har sun kutsa cikin ƙasar, jami’an gwamnatin birnin Addis Ababa na ƙaryata duk wani labarin kasancewar dakarun Habashan a Somaliya.
Shaidu da yawa ne dai suka faɗa wa maneman labari cewa, sun ga ayarin motocin dakarun Habashan sun kutsa cikin harabar Somaliyan, har zuwa ƙauyukan Sariirale da Baragaha da ke kusa da iyakarsu, a ɓangaren Somaliyan, inda suka umarci mazauna waɗannan ƙauyukan da su fice daga nan zuwa wasu yankuna da ke cikin Habshan don kare kansu. Kawo yanzu dai, ba a san burin da sojojin Habashan suka sanya a gaba a wannan ɗaukin ba.
Da yake amsa tamabayoyin maneman labarai a wata fira da ya yi da gidan rediyon Deutsche Welle, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Habashan, Wahede BELAY, ya ce ƙasarsa ba ta da dakaru a Somaliyan. Sai dai wasu masu horas da aikin soji ne ta tura can don su taimaka wa gwamnatin wucin gadin ƙasar wajen horad da sojojinta. Ya dai ƙara bayyana cewa:-
„A kowace shekara, kamar yadda gwamnatinmu ta sha nanatawa, wata tawagar horaswa kawai muke turawa a Somaliya, inda gwamnation wucin gadin ke da cibiyarta. Wannan dai shi ne matsayin gwamnati. Ba ma yaƙi a cikin Somaliya. Duka wasu labarai game da hakan, wato farfaganda ce kawai da jami’an ’yan tsagerun ƙungiyoyin kotunan islama na Somaliyan ke yi don shafa wa sunan Habasha kashin kaza.“