Hali na rashin tabbas ga makomar Burkina Faso
September 22, 2015A daidai lokacin da shugabannin Kungiyar ECOWAS ke gudanar da wani taro na neman shawo kan rikicin kasar Burkina Faso, sojojin da suka yi juyin mulkin na ci gaba kin amsa tayin da sojojin da ke biyayya ga gwamnati suka yi masu na su mika wuya. Sai dai jagoran masu juyin milkin Janar Diendere ya ce ba su fatan ta kaisu ga fada da takwarorin nasu kuma a shirye ya ke ya mika mulkin bisa tanadin da shugabannin kasashen Kungiyar yammacin Afirkan bayan taronsu na Abuja.
An dai share tsawon yinin Talata a birnin na Ouagadougou ana kallon kallo tsakanin sojijin rundunar RSP din da suka yi juyin milkin da kuma sauran sojojin da ke biyayya ga gwamantin rikon kwarya inda ko wanne ya ja daga dauke da manyan makaman yaki. Sai dai a wata fira da ya yi da gidan Radiyon DW jagoran masu juyin milkin ya ce ba ya fatan ta kaisu ga gwabzawa tsakaninsu da takwarorin nasu.
"Ya ce ba mu fatan yin fada domin ba shi ne mafita ba. Za mu ci gaba da tattaunawa wacce na ke ganin ita ce hanya mafi kyau. Ai mu dukkanninmu yan uwa juna ne dan haka ba alkhairi ba ne mu kai ga bugawa tsakaninmu"
Takardun da ke barazanar yin fallasa na tasiri a rikicin
Sa'o'i sama da biyar ke nan dai da wa'adin da aka baiwa masu juyin milki na su mika wuya ya kawo karshe kuma al'ummar birnin na Ouagadougou na ci gaba da zaman jiran abunda ka iya biyo baya. Malam Nafi'ou Mohamed wani Dan garin Sokoton Najeriya ne da ke aiki a birnin na Ouagadougou, kuma ya yi mana karin bayani dangane da halin da birnin ya ke ciki a halin yanzu.
Da ta ke tsokaci kan halin da kasar ta Burkina ta ke ciki a halin yanzu, uwargidan tsohon shugaban kasar Thomas Sankara wato Mariam Sankara ta bayyana tsayiwar gwamnatin jaki da tsoran da ya ke da, na fuskantar shari'a musamman ganin irin yanda wani rahoton bincike da aka bayyana kan irin ta'asar da mulkin gwamnatin Compaore ta aikata a tsawon shekaru 27 na mulkinsa. Sannan ta ce tana kyautata zaton Janar Diendere na da hannu a cikin kisan mai gidan na ta marigayi Thomas Sankara.