Har yanzu ana cikin halin rashin tabbas a Burkina Faso
September 21, 2015Rundunar sojojin kasar Burkina Faso ta ce dakarunta na dannawa Ouagadougou babban birnin kasar da nufin kwance damarar sojojin da ke da hannu a juyin mulkin makon da ya gabata. Hakan dai na zuwa ne daidai lokacin da zaman dar-dar ke karuwa a kasar. Wata sanarwa da aka danganta ta da shugabannin sojojin kasar ta ce manufar dakarun ita ce kawar da jagororin juyin mulkin daga mukamansu ba tare da an zubar da jini ba. Sai dai wannan matakin na sojojin na barazanar kara dagula al'amura a kasar, wadda da ma ke cikin halin rashin tabbas. Sojojin da suka kwace mulki a makon da ya gabata na sashen masu tsaron fadar shugaban kasa ne wadanda ke biyayya ga tsohon shugaba Blaise Compaore, sannan janar dinn da aka nada mukamin shugaban kasa tsohon na hannun damar Compaore ne.