Haramcin zirga-zirgan dare a iyakokin Burkina Faso da Mali
March 9, 2017Talla
Gwamnan ya ce hanin ya shafi duk wasu masu motoci, ko babura, har ma da masu laulawa ko keke. Kuma yana somawa ne tun daga misalin karfe biyar na yammaci zuwa karfe shida na safe. Sanarwar ta Burkina Faso ta ce wannan hani ya shari yankuna kamar na Baraboule, Nassoumbou, Koutoukou, Deou, Oursy, da kuma Markoye dukanninsu da ke a iyakan kasashen biyu na Burkina Faso da Mali a yankin arewacin kasar ta Burkina Faso.
Kasar ta Burkina Faso dai ta fuskanci hare-hare a 'yan lokuttan baya-bayan nan daga 'yan ta'adda da ke fitowa daga kasar Mali, wanda kuma take ganin yin hakan, shi ne zai iya taimakawa wajen kawo karshen hare-haren da take fuskanta.