Hare-hare a Somaliya
November 5, 2007Talla
Aƙalla `yan Somalia 2 ne su ka rasa rayukansu a lokacinda sojojin Habasha suka maida martani kan wani hari da aka kaiwa tawagarsu a kusa da birnin Mogadishu.Waɗanda su ka gane wa idonsu sunce sojojin sun buɗe wuta ne kan wasu mutane da su ke wucewa,haka kuma sojojin na Habasha sun toshe hanyoyi tun bayan wannan hari.Dubban yan kasar Somalia ne suka rasa rayukansu cikin rikicin ƙasar ta Somalia.