1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren ta'addanci a Burkina Faso

Salissou BoukariJanuary 16, 2016

Jami'an tsaro masu yaki da ta'addanci na Burkina Faso, da ke samun tallafin dakarun kasar Faransa, da na Amirka, sun kawo karshen harin 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/1Hea2
Hoto: Getty Images/AFP/A. Ouoba

Rahotanni daga Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso na cewaR, a kalla mutane 20 ne suka rasu sakamakon wani harin ta'addanci da aka kai a wani otel da ke tsakiyar birnin, inda akasari 'yan kasashen waje ne suka fi sauka a cikin sa. Shaidun gani da ido dai sun ce wasu mutane ne masu fuskoki a rurrufe suka kai wannan hari dauke da manyan makammai inda suka yi garkuwa da mutane da dama, inda kuma bayannan na farko ke cewa an halla mutane a kalla 20 duk kuwa da cewa hukumomin na Ouagadougou ba su bayar da wani adadi ba kawo yanzu.

Burkina Faso Anschlag auf Splendid Hotel in Ouagadougou
Hoto: Getty Images/AFP/A. Ouoba

Sojojin Faransa da na Amirka da ke wannan kasa ne suka dafawa dakarun kasar ta Burkina Faso a wajan shayo kan wannan matsala inda suka samu kubutar da mutane 126 daga cikin hotel din cikinsu mutane a kalla 33 sun samu raununa. Daga cikin wadanda aka kubutar din har da Ministan ma'aikata na kasar ta Burkina Faso Clément Sawadogo da ke cikin wannan Hotel lokacin da aka kai hari.

Burkina Faso Anschlag auf Splendid Hotel in Ouagadougou
Hoto: Reuters

A wani bayani da ya yi, ministan yada labaran kasar ta Burkina Faso Simon Compaoré ya ce dakarun nasu sun kashe 'yan ta'addan guda uku wadanda suka kai harin cikinsu balarabe daya da kuma babbaku guda biyu kuma harin ya kawo karshe karshe bayan da aka shafe tsawon a kalla Sa'o'i bakoye ana jan daga.

Sai dai kuma jami'an tsaron masu yaki da ta'addanci sun ci gaba da bincike a wani otel din da ake kira Ybi da ke kusan Cappuccino inda ake tsammanin wasu 'yan bindigan sun makale a ciki. Kungiyar AQMI ta Al-Qaida a yankin Sahel ce ta dauki alhakin kai wannan hari.