1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren ta'addanci a Somaliya

February 21, 2014

Kungiyar Al-Shabab ta Somaliya dake da alaka da kungiyar al-Qaeda ta dauki alhakin kai harin kunar bakin waken da aka kai da mota a fadar gwamnatin kasar.

https://p.dw.com/p/1BDcO
Hoto: picture alliance/AP Photo

Kakakin kungar ta al-Shabab Sheikh Abdul Aziz Abu Musab ne ya sanar da hakan, inda yace harin da suka kai a fadar shugaban kasar dake Mogadishu sun kai shi ne da niyyar kashewa ko kuma kame dukkan jami'an gwamnatin da ke wajen.

Harin bama-bamai da aka kai da mota a gaban fadar shugaban kasar Somaliya dake Mogadishu babban birnin kasardai ya hallaka a kallah mutane 16 tare kuma da jikkata wasu da dama. Rahotannin farko da aka bayar sun bayyana cewa akallah dakarun gwamnatin kasar 10 ne da kuma tsagerun kungiyar ta al-Shabab shida suka rasa rayukansu yayin harin.

Sai dai kuma ministan tsaron kasar Abdikarim Hussein Gulled yace babu abin da ya samu Shugaba Hassan Sheikh Mohamud haka nan ma babu wani jami'in gwamnati da ya rasa ransa ko kuma ya samu rauni yayin wanna harin, ya kara da cewa a yanzu haka al'amura sun koma kamar yadda ya kamata a fadar shugaban kasar.

Somaliya dai ta kwashe tsahon shekaru da dama tana fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyar ta al-shabab ta masu kaifin kishin addini.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar