Hare-haren ´yan tawaye a Somaliya
December 13, 2007Talla
Mutane tara a birnin Magadishu na ƙasar Somaliya sun rasa rayukansu.Hakan nada nasaba ne da wani hari da ´yan tawaye su ka kaine a kasuwar Bakara. Kafin kai harin, sai da ´yan tawayen su ka yi taho mu gama da sojin ƙasar, dake samun tallafin sojin Habasha. Rikicin ´yan tawayen a yanzu haka ya yi sanadiyyar rayuka da daman gaske a ƙasar. Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun ce a shekarar nan, mutane kusan dubu shidda ne su ka rasa rayukansu. Ywaitar rikice-rikice a ƙasar ya haifar ´yan Somaliya ci gaba da yin hijira, don tsira da rayukan su izuwa maƙotan ƙasashe.