Hare-haren ƙunar baƙin wake a Somaliya
July 5, 2014Talla
A ƙalla mutane huɗu ne suka mutu , yayin da wasu fiye da goma suka jikkata, a sakamakon harin ƙunar baƙin wake da aka kai cikin wata mota mai shaƙe da bamai-bamai, a wannan Asabar ɗin din (05.07.2014) kusa da zauran majalisar dokokin da ke a babban birnin ƙasar na Somaliya.
Tuni dai Ƙungiyar Al-Shebaab ta ɗauki alhakin kai wannan hari, wanda shi ne irinsa na farko tun soma azumin watan Ramdan. Kakakin 'yan sandar ƙasar Qasim Ahmed Roble, ya tabbatar da harin wanda ya ce daga cikin waɗanda suka mutu har da 'yan sanda guda biyu, sannan kuma mafi yawan waɗanda suka jikkata a ƙalla mutane 13, fararan hulla ne.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hasane