1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a Somaliya ya kashe mutane sha huɗu

September 20, 2012

Wani ɗan harin ƙunar bakin wake ya tarwatsa bom a wajen wani cin abinci da fitattun 'yan jarida da kuma 'yan siyasa ke yawan zuwa Mogadishu, fadar gwamnatin Somaliya.

https://p.dw.com/p/16C6j
Somali government soldiers patrols the scene of an explosion in capital Mogadishu September 12, 2012. Somalia's al Shabaab rebels carried out a bomb attack on Wednesday that targeted a Mogadishu hotel where the president and Kenya's visiting foreign minister were holding a news conference, the group said. REUTERS/Omar Faruk (SOMALIA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS SOCIETY)
Hoto: Reuters

Harin na Mogadishun wanda aka kai shi a Alhamis ɗin nan ya yi sanadiyyar rasuwar mutane goma sha huɗu kamar yadda babban jami'in rundunar 'yan sandan birnin na Moghadishu Kanar Mohammed Dahair ya shaidawa manema labarai, sai dai ya ce kawo wannan lokacin ba su tantance ko mutane nawa ne su ka jikkata ba.

A tasa zantawar da manema labarai, Abdiwali Hassan da ke zaman ɗaya daga cikin jami'an 'yan sandan na Mogadishu ya ce daga cikin waɗanda su ka rasu har da wasu 'yan jaridu guda uku sai dai bai tantance ko harin ya haɗa da manyan 'yan siyasar ƙasar ba.

Tuni dai aka fara zargin ƙungiyar nan ta al-Shabab da ke gwagwarmaya da makamai da alhakin kai hari, sai dai kawo yanzu ƙungiyar ba ta ce uffan ba.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman