SiyasaAfirka
Hari ya halaka mutane uku a Somaliya
March 15, 2024Talla
Mutane uku suka halaka yayin da wasu kusan 30 suka jikata sakamakon harin da aka kai kan wani otel a birnin Mogadishu fadar gwamnatin Somaliya cikin dare, kamar yadda mai magana da yawun 'yan sanda ya tabbatar.
Tuni jami'an tsaro suka yi kawanya ga wannan otel da jami'an gwamnati ke amfani da shi, kuma tuni tsagerun kungiyar al-Qeada suka dauki alhakin kai harin na Somaliya.