Hari ya hallaka sojoji a Burkina Faso
June 12, 2020Talla
Akalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da ake zargin mayaka ne masu da'awar jihadi ne, suka kai hari a kan sojoji da ke iyakar kasashen Ivory Coast da kuma Burkina Faso.
Harin wanda ya auku cikin daren da ya gabata, ya kuma jikkata wasu mutum shida a cewar wasu majiyoyin soji da ke a yankin Kafolo da abin ya faru a ciki.
Wani babban jami'in soji a yankin, Lassina Doumbia, ya ce za a kaddamar da hare-hare ta sama cikin 'yan kwanakin da ke tafe, saboda tsaurara tsaro.
Babu dai wata kungiyar da ta dauki alhakin lamarin ya zuwa yanzu, sai dai jami'ai na cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.