1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari ya ritsa da 'yan majalisan Somaliya

May 1, 2012

Harin ƙunar bakin wake ya salwantar da rayukan mutane shida ciki har da ''yan majalaisar dokokin Somaliya, a lokacin wata zama ta samar da gwamnatin tsakiya.

https://p.dw.com/p/14nfg
Soldiers stand guard outside the national theatre after an explosion, in Mogadishu April 4, 2012. Al Shabaab rebels in Somalia claimed responsibility for the explosion that killed at least six people and wounded some government officials. REUTERS/Feisal Omar (SOMALIA - Tags: TPX IMAGES OF THE DAY CIVIL UNREST)
birnin Mogadischu ma bai tsira daga hare-hare ba.Hoto: Reuters

Mutane shida sun rasa rayukansu a Somaliya ciki kuwa har da 'yan majalisa biyu lokacin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya ƙaddamar da hari a Dhusamareb da ke tsakiyar ƙasar. Akasarin waɗanda suka kwanta da dama sun zo halartar zaman tattaunawa ne tsakanin gwamnati da wasu masu tsananin kishin addini da suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu a baya.

Babu dai wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin wannan harin na Dhusamareb. Sai dai tun watannin biyun da suka gabata, Al-Shabab ta lashi takobin mayar da garin ƙarƙashin ikonta, bayan da ƙungiyar Ahlu Sunna wal Jama'a da yanzu ke ƙawance da gwamnati ta karɓe shi a watan maris.

Wannan harin dai ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin riƙon ƙwaryar Somaliya da ma dai MDD suka nuna damuwa, game da aniyar da masu tsananin kishin addini suka bayyana, na yin ƙafar ungula ga shirin samar da tsayeyyar gwamnati. Tun a watan satumban bara ne gwamntin riƙon ƙwarya ta Somaliya da kuma ƙungiyar Ahlu Sunna wal Jama'a da kuma wasu sarakunann gargajiya suka amince su jere tare, kana su kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa kan nan da watan Agusta mai zuwa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman shehu Usman