Kungiyar Al-Shabaab ta kai hari a Somaliya
December 15, 2016Talla
Wanda ya kai wannan hari dai, ya dana bam din ne a karkashin wata itaciya inda sojojin su ke a wani wuri da ke wajen birnin Mogadishu a cewar Abdifatah Omar Halane, mai magana da yawun hukumomin birnin, wanda kuma ya ce wasu sojojin da dama sun samu raunuka.
Sai dai tuni Kungiyar Al-Shabab ta bakin daya daga cikin kakakinta Abdiasis Abou Moussab, ta dauki alhakin kai wannan hari, sannan ta ce sojojin da suka mutu sun kai 10. Shaidun gani da ido sun ce tashin bam din na farko ya tarwatsa wani gidan cin abinci da ke wurin kafin daga bisani maharan su buda wuta.