Harin jiragen yakin Amurka a Somaliya
March 14, 2016
Zamu bude shirin ne da sharhin da jaridar Berliner Zeitung ta yi kan hare haren da jirage marasa matuka na Amurka suka kai a kan 'yan al-Shabaab a kasar Somailiya. Jaridar ta cigaba da cewar, a wani mumman hari da jiragen yakin Amurka marasa matuka suka kai a Somali, mayakan tsagerun kungiyar Al-Shabaab 150 suka bakunci lahira. Jiragen sun kai somame ne a yankin arewacin babban birnin kasar watau Mogadishu, a wani sansani na horar da mayakan da ake kira Raso, inda aka lalata sansanin baki dayansa.
Kakakin fadar gwamnatin Amurka ta white house Jeff Davis, ya sanar da cewar mayakan da ke da alaka da kungiyar Al-Qaeda, suna mataki na karshe ne na samun horo a shirinsu na kai hare haren ta'addanci, a lokacin da jiragen yakin Amurkian suka afka musu.
Davis ya kara da cewar, dakarun Amurka sun dade da sanyawa wannan yanki idanu. Kuma an yi imanin cewar za'a turasu ne yankunan daban daban domin kai hari, bayan samun wannan horo na musamman. Sai dai kawo yanzu babu tabbacin ko harin ya ritsa da manyan jami'ansu. Akwai tabbacin cewar harin bai ritsa da fararen hula ba. Kakakin Al-Shabaab ya tabbatar da somamen sai dai ya ki cewa komai game da yawan wadanda suka rasa rayukansu.
Daga batun somame akan mayakan al-Shabaab a Somali sai kuma matsalar yunwa an kasar Ethiopia da ke makwabtaka. Jaridar Die Tageszeitung ta ce ga kasa da tattalin arzikinta ke bunkasa, amma kuma miliyoyin al'ummarta na cikin halin tsaka mai wuya na yunwa, ba domin matsalar yanayi na fari ba har ma da irin tsarin da gwamnatin kasar ke yi wa al'umma.
Jaridar ta ci gaba da cewar, shekaru bakwai da suka gaba anga yadda mutane ke layi a garin Lalibela, suna karbar tallafin abincin da za su ci daga wajen jami'an kananan hukumomi da na kungiyar tallafi na kasar Amurka watau USAID. A wannan lokacin dai ana dab da shiga damuna ce. Yanzu wanna al'umma ta Lalebela da ke da tarihin tsoffin majami'u, sun sake tsintar kansu cikin hali mawuyaci na rashin abinci sakamakon fari.
Ga gwamnatin Ethiopian dai matsalar karancin abunci abun kunya ne. Dangane da haka ne ma hukumomin wannan kasa da ke yankin gabashin Afirka ke tsare baki masu yawon bude ido da ke daukar hotunan mutanen da ke tagayyara saboda yunwa.
It kuwa jaridar Süddeautsche Zeitung tsokaci ta yi game bukin kewayowar ranar haihuwar tsoho mai dogon zamani kuma mai mulkin sai madi ka ture a Afirka watau shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe. Jaridar ta ce liyafa ce babba, inda baki dubu 50 suka yi tururuwa zuwa yankin kudancin Zimbabwe, domin tayashi murnar kewayowar wannan rana.
A karshen watan Febrairu ne dai aka yi bukin cikan Mugabe shekaru 92 da haihuwa, da bolon bolon 92 da babban Cake mai nauyin kg 92, da wakoki da kade kade. Tare da mai dakinsa Grace mai shekaru 40 da haihuwa, Mugabe mai dogon zamani ya yi ta karbar gaisuwar taya murna kafin ya sanya cake din da aka yi da launuka kala kala a bakinsa.
Mugabe da ke mulkin kasar tun samun 'yancin kai a shekarata 1980, ya yiwa dokar mallakin filayen noma a kasar gyaran fuska a shekarata 2000, inda aka kwace gonaki daga hannun fararen fatar kasar aka rarraba wa bakake, wadanda basu da masaniya dangane da noman zamani a manyan filayen gonaki.