1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake a Somaliya.

March 17, 2014

Kungiyar Shebab ta kasar Somaliya ta kai wani sabon harin kunar bakin wake ga jerin motocin dakarun AMISOM dake ayukan tsaro a wannan kasa.

https://p.dw.com/p/1BRCi
Hoto: Mohamed Abdiwahab/AFP/Getty Images

Wani sabon harin kunar bakin wake da aka kai a wannan Litinin din (17.03.2014) nan a kusa da birnin Mogadishu, yayi sanadiyar mutuwar a kalla mutane bakwai, cikin su kuwa har da baki yan kasashen waje a cewar Abdiaziz Abu Musab, kakakin kungiyar Shebab da ta dauki alhakin kai harin.

Harin dai an kai shi ne ga jerin motocin dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka na AMISOM dake ayukan tsaro a wannan kasa.

A cewar Abdulahi Mohamed wani da ya ganema idanun sa yadda aka kai wannan hari, yace harin ya wakana ne a wata hanya da ta hada Afgoye da Mogadisho babban birnin kasa, bayan da wani dan kunar bakin wake ya fada da motar sa cikin jerin motocin dakarun na Amisom, sannan kuma yace tuni yaga motocin agaji na soja sun nufi wurin a guje.

Saidai a sanarwar da ta fitar ne jim kadan bayan harin, kungiyar ta Shebab tace itace ta kai wannan hari.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba