Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 10 a Somaliya
April 21, 2015Talla
Wani dan harin kunar bakin wake ya hallaka kimanin mutane 10, lokacin da ya tashi bam cikin mota a wajen cin abinci mai cike da mutane da ke tsakiyar birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar Somaliya. Harin na wannan Talata an kai shagon cin abinci da ma'aikata ke zuwa.
'Yan sanda sun ce akwai yuwuwar samun karin wadanda za su halaka saboda akwai wadanda suka samu munanan raunika. A jiya Litinin wani hari kan ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya ya kai ga mutuwar mutane bakwai. Ana daura alhakin hare-haren da ake samu a kasar ta Somaliya kan tsagerun kungiyar al-Shabaab masu kaifin kishin addinin Islama.