Harin ta'adanci a Burkina Faso
December 2, 2019Talla
A wata sanarwar da gwamnan yankin da abun ya faru ya fitar, ya yi Allah wadai da harin inda ya kuma kara da cewar al'ummar yankin da su tashi tsaye don lura da ire-iren mutanen da ke kai kawo a yankin.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin wannan harin. Amma ana zargin mayakan jihadi da suka yi kaurin suna a kai hare-haren ta'addanci a kasar da hannu a harin.