1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ƙunar baƙin wake a Somaliya

Umar Saleh SalehAugust 24, 2010

Mutane 31 cikin har da 'yan majalisa sun rasa rayukansu a harin da ƙungiyar Al-Shabbab ta Somaliya ta kai a birnin Mogadishu.

https://p.dw.com/p/Ouw8
Hoto: AP

Wani hari da masu tayar da ƙayar bayan Somaliya suka kai a wani Hotel da ke kusa da fadar shugaban ƙasa a Mogadisho, ya haddasa mutuwar mutane akalla 31 ciki kuwa har da 'yan majalisa da dama. Ma'aikatar yaɗa labaran ƙasar ta Somaliya ta ce wasu masu tsananin kishin addini da ke sanye da kakin soja ne suka yi luguden wuta akan waɗanda ke cikin wannan hotel, yayin da na ukun su ya tayar da bam da ya ke riƙe da shi.

Wannan harin ƙunar baƙin wake ya zo ne kwana guda bayan ɓarkewar faɗa tsakanin dakarun gwamnatin Somaliyar, da kuma masu tsananin kishin addini da ake yi wa laƙabi da Al-Shabbab. ƙungiyar ta Al-Shabbab da kashi 90% na ƙasar ta Somaliya ke hannuta, ta na nuna adawa da ƙarin sojojin wanzar da zaman lafiya da Au ta tura wannan ƙasa. Dakaru 6.000 ne suka isa ƙasar ta Somaliya da nufin mara wa dakarun gwamanti baya a fito na fito da suke yi masu tayar da tarzoma.

Tun a a shekara ta 2007 ne dai, ƙungiyar Al-Shabbab mai alaka da ƙungiyar Al-Qa'ida ke yaƙi da gwamnatin riƙon ƙwaryar Somaliya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala