Hasashen masana kan sauyin yanayi
November 12, 2013Maukaciyar guguwar da yanzu haka ke kaɗawa a yankin Asiya, wanda kuma ta yi mummunar ɓarna a ƙasar Philippines, inda mutane da dama su ka mutu. Wannan guguwar mai ƙarfi, an ji kadawarta har a ƙasashen gabashin Afirka da ke gaɓar Tekun Indiya, kamar misali ƙasar Somaliya. Masana sun bayyana cewa babban dalilin irin wannan mahaukaciyar guguwa shi ne, sauyin yanayi.
A fadar masanin kimiyar yanayi da ke ƙasar Jamus, Christian Herold, ya ce a shekarun da suka gabata babu wani babban mataki na bin tsarin da aka yi, bisa sauyin yanayi, inda aka mai da hankali kawai bisa bayanan da taurraun ɗan Adam ke bayarwa.
"Ba'a bi diddigin lamarin yadda ya kamata ba, don haka binciken da aka gudanar ya yi kaɗan. A 'yan shekarun da suka gabata mun fara yin amfani da taurarun ɗan Adam"
Mahaukaciyar guguwa kamar ta Horricane, Taifun da dai sauransu, irin waɗannan bala'o'i da ake samu a yancin hamada suna matuƙar buƙatar binciken masana da gwaji ɗaya izuwa sau biyar. Masana suka ce idan an yi bincike mai zurfi kamar haka ne, za su iya sanin ta ina iskar za ta taso, kana ina da ina za ta shafa, kana su na iya yin ƙiyasin ɓarnar da za ta iya haddasawa. Friedrich Wilhem Gersterngarbe da ke cibiyar kula da mahalli a Postadam a ƙasar jamus ya yi ƙarin haske.
"Irin wannan mahaukaciyar guguwa da ke kaɗawa a Phillipines yanzu haka, a ƙashin gaskiya ba mu maida hankali a kanta b, inda ta ke gudun kilo mita 300 a sa'a guda. Gudun iskar abu gudane, sannan kuma guguwar ta haddasa ambaliyar dama-damai da koguna. Akwai mummunar ɓarna da ambaliya ta yi"
Masana daban-daban dai sun sha bayana cewa, bincikensu ya nuna alamar samun ƙaruwar sauyin yanayi, wanda kuma a 'yan shakarunnan aka ga yadda yake haddasa bala'o'i a ƙasashen duniya, musamman waɗanda ke gaɓar ruwayen teku.
"Akwai yankuna da dama, waɗanda zafin ruwan tekunansu ya ƙaru. Ciki harda yankin Karibiyan, inda wannan guguwar Taifun ta faro. A wannan yankin zafin ruwayen tekunansu yakan kai maki 30 a ma'aunin zafi. A da kuwa bai wuce maki 27 izuwa maki 28"
Wata babbar matsala da ta fi kasance wa masanan kimiyar yanayi gagara badau shi ne, yadda ba da safai su ke iya sanin haƙiƙanin wace irin iska za a yi ba, kuma wane irin nau'in za ta bullo ba. Don haka ko da sun yi bincike, sau tari akan samu bala'in da ke aukuwa ya saɓa da tunaninsu.
Yanzu dai abin da ya ragewa gwamnatocin duniya shi ne, shin ko za su ɗau ƙwararan matakai na kare mahalli, ta inda za a tsawatar wa masana'antu wajen rage fidda hayaƙi masu sa guba?. Ko kuma duniya ta ci gaba da kasan cewa cikin hatsari na aukuwar bal'a'o'i, waɗanda ke samun asali daga sauyin yanyi.
Mawallafa: Brigitte Osterath/ Usman Shehu Usman
Edita: Pinado Abdu