Kyamar mika masu aikata laifi a China na kamari a Hong Kong
July 9, 2019Talla
Shugabar gwamnatin yankin Hong Kong Carrie Lam ta bayyana a wannan Talatar da cewa kudirin dokar nan da aka shigar gaban majalisa da ya janyo da kazamar zanga-zanga ya mutu murus.
Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce Carrie Lam, ba ta fito fili ta yi bahasi kan ko janye dokar ne aka yi kwata-kwata ba, batun da kuma ya kara haifar da fargaba da ma harzuka masu zanga-zangar da ke nuna kyama game da dokar.
A yayin wani taron manema labarun da ta jagoranta Missis Lam ta ce a shirye ta ke da ta gana da kungiyar daliban kasar da ke boren a bainar jama'a ba tare da gindaya wani sharadi ba, batun da kuma masu zanga-zangar suka yi watsi da shi tare da kiran wani sabon gangami.