1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HRW ta ce ana sa yara aikin soja a Somaliya

February 22, 2012

Kungiyar Human Rights Watch ta zargi ɓangarorin da ke gaba da juna a rikicin Somaliya da sa yara aikin soja,tare da yi wa yaran mata auren dole.

https://p.dw.com/p/147cz
A young Alshabab soldier prepares to join fighting between Alshabab and Ethiopian forces near the presidential palace in Mogadishu, Somalia on 12, January 2009. Islamic fighters launched heavy attacks on two Ethiopian bases on the eve of Ethiopian expected withdrawal from Somalia. EPA/BADRI MEDIA +++(c) dpa - Report+++
Birnin Mogadischu na daga cikin wuraren da aka samun yara soja.Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan rahoton na human Rights Watch mai shafi 104 , ya na bayyani ne dalla dalla game da hanyoyin da ake bi domin tilasta wa yara ƙanana shiga aikin soje a Somaliya a cikin shekaru biyu na baya-bayannan. ƙungiyar da ta himmatu wajen kare hakkin bil Adama a ko ina cikin duniya, ta dogara ne kan wasu hirarraki 164 da ta yi da yaran na somaliya, ciki kuwa har da 21 da suka yi nasarar tserewa daga hannun 'yan Al-Shabab wajen kafa hujjojinta.

Somali children enjoy a liquid food drink provided by a local NGO in the port town of Kismayo, Wednesday, Sept. 12, 2007, where more than eight thousand Children live in camps. The Somali health minister and UNICEF warned on Wednesday that thousands of children were facing starvation as violent attacks continued around the south of the country, "We have been receiving reports of an alarming rate of malnutrition in southern Somali regions, where thousands of children are on the verge of death," said Health Minister Isse Weheliye. (AP Photo/ Nasteh Dahir Farah)
yxara ba su da galihu a Somaliya.Hoto: AP

HRW ta nunar da cewa tun bayan rintsaɓewar yaƙin Somaliya tsakanin sahekara ta 2010 zuwa ta 2011, ƙungiyar Al-Shabab ta tilasta ma yara ƙanana, ciki har da waɗanda suke da Ƙasa da shekaru 10 da haihuwa, ɗaukan makamai domin shuga fagen yaƙi da suke yi da gwamnati. Hasali ma dai, wasu daga cikin yaran na somaliya ne ke ƙaddamar da hari ne na ƙunar bakin wake. ƙungiyar ta kuma nunar da cewa Al-Shabab na sace yaran mata da nufin tilasta musu yin wasu aikace aikace na gida, tare da ɗaura musu auren dole da wasu daga cikin 'yayan ƙungiyar. kana ta na barazanar ɗaukan tsauraran matakai da ke kai wa ga kisa akan duk wacce ta kuskura arcewa.

A cewar Tirana Hassane, jami'ar Human Rights Watch da ke kula da bincike game da batutuwa masu sarƙaƙiya, wannan tauyen hakkin yara, zai daƙushe makomar ƙasar ta somaliya baki ɗaya.

"Yaran sune manyan gobe na Somaliya. Amma kuma ba wasu matakai da ake ɗauka domin kare su. Ma'ana a kuɓutar da su daga ayyukan soje da makamantansu. Rashin sauke wannan nauyi, ba a kansu kawai zai iya tasiri ba, amma ya na barazanar ne ga makomar ƙasar baki ɗaya."

Ita dai ƙungiyar ta HRW ta ce dakarun gwamnati riƙon ƙwaryar Somaliya ma ba a barsu a baya ba, wajen tursasa wa yara ƙanana a ƙasar. Hasali ma dai ƙungiyoyin sa kai da suke mara wa gwamnati baya suna sanya yara a sahun gaba a filin daga.Ma'ana suna zame musu garkuwa a fagen yaƙi. Saboda haka ne Tirana Hassana , jami'ar HRW, ta ce yara ba su da galihu ko kaɗan a Samaliya,

"Somaliya, ɗaya daga cikin ƙasashe ne na duniya da ba a kiyaye hakkin yara. A fannin ilimi ga misali, ta na ɗaya daga cikin wuraren da ake samun ƙarancin yara da suka iya karatu da rubutu. kana yara na cikin barazanar a ko wani lokaci. Idan sun sami zarafin zuwa makarata, su na tattare da tababa. A takaice dai, ga yaro abu ne mai wahalan gaske samun ilimi, ko kuma samun rayuwar da ta dace."

ARCHIV - Junge Kämpfer der sogenannten Union Kongolesischer Patrioten (UPC) beim Schusstraining am Rande von Bunia (Archivfoto/Illustration vom 14.6.2003). Der US-amerikanische Nachwuchsautor Uzodinma Iweala ist für seinen Roman "Du sollst Bestie sein" in die Haut des afrikanischen Kindersoldaten Agu geschlüpft. Der Junge erzählt aus dem Leben in der Rebellentruppe, wie er Dörfer niederbrennt, Menschen niedermetzelt, Frauen vergewaltigt. Killen wird zu seinem Lebensinhalt. Er tut es nicht gerne, aber er tut es ohne Mitleid. Foto: Maurizio Gambarini dpa (zu dpa-Literaturdienst vom 11.02.2008) +++(c) dpa - Bildfunk+++***Zu Ripperger, Red Hand Day 2008 - Kampagne vom "Deutschen Bündnis Kindersoldaten"***
Kwango ma na sa yara aikin soja.Hoto: picture-alliance/ dpa

Ita dai ƙungiyar Human Rights Watch ta yi kira ga ɓangarorin da ke da hannu a rikicin Somaliya, da su yi wa Allah da ma'aiki, su daina tursasa wa yara ƙanana. Kana ta bukaci ƙasashen duniya da su ɗauki matakan da suka wajaba domin raba yaran Somaliya da cin zarafi da kuma baƙar azaba da gwamnati da kuma al-Shabab ke gana musu a fagen yaƙi da ya yi kaca-kaca da Somaliya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu