1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar abinci ta duniya wato WFP ta ce ba ta da fargaba akan rabon abinci a Somaliya

August 16, 2011

Wasu ƙungiyoyi masu zaman kan su na baza labarin cewa ana soce kayan agajin na abinci da ake ƙai wa Somaliya

https://p.dw.com/p/12HON
Rabon abinci ga jama'a a SomaliyaHoto: dapd

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta yi gargaɗin cewa kayan abince na agaji da ake aike wa ga waɗanda fari ya shafa a ƙasar Somaliya na isa ga jama'ar da ake aike wa dan su.Wata mai magana da yawun hukumar Christiane Berthiaume da ke mayar da martannin a wani taron manema labaran da ta kira bayan da ƙungiyoyi masu zaman kan suka riƙa baza labarin cewa an fara soce kayan abinci.

Ta ce hukumar ba ta da wani fargaba ko shaku akan isar agajin ga jama'ar, kuma ta ce zasu gudanar da bincike domin gano ko an yi soce socen.Yazuwa yanzu sama da mutane miliyion ɗaya ne da rabi suka samu agajin a yankunn tsakiya da na arewacin Somaliyar kamar yadda hukumar ta WFP ta sanar.mutane kusan miliyion 12 ke fama da matsalar yunwa a kusrwar Afrika sakamakon fari da kuma yaƙe yaƙen da ake fama da su.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman