Sabon tsarin sake rubuta jarrabawa a Najeriya
January 6, 2025Ita dai wannan jarrabawa ana rubutawa ne daga cikin kasashen wannan yankin na Africa inda kowace kasa ke bada tallafi domin cimma manufar da aka sanya a gaba. A sakamakon wannan jarrabawa ta shekarar datac shude kuwa a cewar shugaban hukumar a Nigeria Mr Amos Dagut na cewa an samu nasara.
Karin Bayani: Najeriya: Kasa mafi yawan yara da ba sa makaranta
Kamar yarda wannan sabon tsarin ya nuna cewa dalibai za su iya sake rubuta duk darasin da suka fadi cikin kankanen lokaci ba sai shekara ta zagayo ba inji kakakin hukumar ta WAEC, wanda ya ce hukumar ta samar da sabon tsari ne na sake zana jarrabawa ga wadanda suka fadi darasi daya ko biyu cikin kasa da wata biyu wanda a yanzu an fara yin rijistar jarrabawar a ofisoshin hukumar da ke kowace jiha ga misali a Najeriya.
Farfesa Abdulrashid Garba tsohon shugaban hukumar jarrabawa ta kasa ne kuma shugaban wata Jami'a mai zaman kanta a Najeriya ya ce da sauran aiki bisa daukar wannan sabon tsari na hukumar ta WAEC, sannan ya nuna muhimmancin kammala tsarin karatun makarantun wanda haka zai rage faduwa jarrabawa. Najeriya dai kasancewar ta uwa ga kasashen Afrika tana yaye dalibai miliyoyi daga makarantun ta a duk shekara.