A Nijar ko allura za ta tono garma a binciken SORAZ?
January 13, 2025A karshen shekara ta 2011 ne dai, jamhuriyar Nijar ta soma aikin hakar arzikin man fetur dinta da aka gano a yankin Agadem na cikin Jihar Diffa. Inda ake hako ganga dubu 100 a kowane yini.
Daga cikin ganga dubu 80 mallakar kamfanin CNPC na kasar Chaina wanda ke aikin man fetur din na Nijar, a yayin da Nijar din ke da ganga dubu 20 wadanda take tacewa a kowane yini a wata karamar matatar mai mai suna SORAZ da ta gina a garin Damagaram.
Ta sayar da ganga dubu 12 a cikin gida ta kuma sayar da rarar ganga dubu takwas ga kasashe makobta irin su Najeriya, Mali da Burkina Faso.
To sai dai shekaru da dama kenan da wasu 'yan kasar ke zargin gwamnatocin mulkin Renaissance na PNDS Tarayya da aikata almundahana a cikin harkar ta man fetur.
Wannan ce ta sanya a yanzu a bisa kiraye-kirayen jama'a, gwamnatin mulkin sojan ta dauki matakin gudanar da bincike kan matatar man fetur din ta SORAZ.
Matakin da Malam Mahamadou Gamatche wani dan fafutika a Nijar ya ce abin a yaba ne da amma akwai bukatar fadada binciken;
''Ba Soraz kawai ya kamata a yi wannan bincike ba. So muke a bar yin tsambare, a fadada bincike tun daga Agadem zuwa Soraz zuwa SONIDEP(Kamfanin dillancin man fetur na kasa).
Gaba dayansu ya kamata a bincika saboda mu san abin da aka saida, abin da aka yi da kudi kuma mi ya yi saura. Bayan wannan kuma kiran da muke ga gwamnati, ba batun man fetur ba kadai, ya kamat duk inda muke da azriki kamar na zinariya a gudanar da bincike,''
Gwamnatocin mulkin jam'iyyar PNDS Tarayyadai sune suka kwashe shekaru sama da 12 suna sarrafa kudaden man fetur din.
kungiyar MOJEN ta bakin shugabanta Malam Siraji Issa na ganin wannan bincike babban kalubale ne musamman ga tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou da ma sojojin da ke mulkin da ya ce allura na iya tono garma.
'' Wannan batu na binciken SORAZ babban kalubale ne ga tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou da ma ministoci biyu da suka jagoranci ma'aikatar man fetur wato Abba dan tsohon shugaban kasar da kuma Foumakoy Gado wadanda dukkaninsu ke tsare.
Amma kuma babban kalubale ne har ga su kansu sojojin da ke mulki da ka iya raba gari da tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou domin kowa ya san harkar man fetur da aKa yi ta akwai fararan hula ciki akwai kuma sojojin da ke mulki yanzu a kasar.”
Yanzu dai ‚yan kasa sun zura ido su ga cibiyar bincike da sojojin za su bai wa wannan aiki.