1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hungary ta saba da dokar EU kan masu hijira

Abdullahi Tanko Bala
May 14, 2020

Yan gudun hijira da ke tsare a sansanin yan gudun hijira a iyakar Hungary na cikin halin tsaka mai wuya yayin da kasashen Hungary da Serbiya suka ki karbarsu

https://p.dw.com/p/3cEAd
Ungarn Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/dpa/L. Witter

Babbar kotun tarayyar Turai ta ce Hungary ta saba doka bisa tsare masu neman mafakar siyasa kamar yan fursuna a wani sansani kusa da iyakar kasar Serbiya.

Wasu yan gudun hijira hudu yan kasashen Iran da Afghanistan suka shigar da karar.

Hukumomin Hungary sun yi watsi da bukatar masu neman mafaka inda suka ce yan gudun hijirar sun shiga kasar ce ta barauniyar hanya daga Serbia, a saboda haka sai dai su nemi mafaka a Serbia amma ba kasar Hungary ba.