Tasirin duba lafiyar hakora ko da lafiya
August 25, 2023Talla
Duba lafiyar hakori lokaci zuwa lokaci abu ne mai kyau da ke kara lafiya wa dan Adam. Saboda bai kamata ba a ce mutum ya tsuffa ba tare da hakoransa ba kamar yadda masana kiwo lafiya suka bayyana. Babu shakka, kula da tsaftar baki na taimaka wa lafiyar hakora. A bisa al'ada, baki yana ƙunshe da adadi mai yawa na ƙwayoyin cuta domin haka tsaftar baki na taimaka wa hakora kansancewa cikin lafiya.