IS ta dauki alhakin kai harin Burkina Faso
December 27, 2019Talla
Kungiyar IS ta bayyana cikin wata sanarwa a wannan Jumma'a cewa reshenta da ke yammacin Afirka na (ISWAP) ne ya kaddamar da harin inda ya tayar da bam a cikin barikin sojan na Burkina Faso da ke Arbinda a lardin Soum da ke arewacin kasar tare da halaka sojoji da dama baya ga jikkata wasu
Burkina Faso na daya daga cikin kasashen yankin Sahel da 'yan ta'adda suka zafafa kai hare-hare musamman ma a barikin sojoji.