1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ingila ta rasa kofinTurai na UEFA

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
July 12, 2021

Ingila da Brazil sun gaza kai bantensu a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai da ta kasashen yankin Latin Amirka wato Copa America

https://p.dw.com/p/3wN0P
EURO2020 I Italien - England
Hoto: Christian Charisius/dpa/picture alliance

A Lahadin karshen mako ne aka fafata tsakanin Ingila da Italiya a filin wasa na Wembley da ke birnin London. Sai dai Ingilan ba ta sha da dadi ba, ko kuma a ce ta ga samu ta ga  rashi. Tun dai a mintina biyu da fara wasan ne, dan wasan baya na Ingilan Luke Shaw ya zira kwallo a ragar Italiya, sai dai a mintina na 67 da fara wasan, dan wasan Italiya Leonardo Bonucciya farke wannan kwallo inda aka kammala mintuna 90 ana kunne doki daya da daya. A karshe dai bayan karin lokaci na mintuna 30, an kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida, abin kuma da ya bai wa Italiyan nasara da ci uku da biyu. 

Barazil ta fadi a gaban Ajantina a kofin Amirka

Fußball Copa America Finale Argentinien - Brasilien
Hoto: Silvia Izquierdo/AP Photo/picture alliance

Shararren dan waasan nan na Ajantina Lionel Messi ya samu nasarar lashe babbar gasa karo na farko ga kasarsa, bayan da Ajantinan ta lashe gasar karshe ta kasashen Latin Amirka wato Copa America. Ajantina dai ta zamo zakara karo na farko cikin shekaru 28 bayan da ta lallasa Brazil a wasan karshe da suka fafata a birnin Rio de Janeiru na Brazil din da ci daya mai ban haushi. Nasarar da Ajantinan ta samu a kan Brazil dai, ta kawo karshen kofin Brazil na sama da shekaru shida da ta kwashe tana samu ba tare da ta yi rashin nasara a gida ba. 

Raja Casablanca ta Moroko ta lashe Kofin confederetion cup

Fußball | FIFA Club-WM - Raja Casablanca - FC Bayern München - 0:2
Hoto: Frank Hoermann/SvenSimon/picture alliance

Raja Casablanca ta Moroko ta lashe Kofin confederetion cup ta kungiyoyin kasashen Afirka bayan da ta doke JS Kabylie ta Aljeriya da ci (2-1) a birnin Cotonou. Minti biyar da fara wasa ne Soufiane Rahimi na Moroko ya zura kwallon farako, kafin daga binasi abokin karawarsa Ben Malongo ya zira na biyu minti tara bayan haka. Amma dai minti daya bayan dawowa hutun rabin lokci ne Zakaria Boulahia na Js Kabylie ya farke daya daga cikin kwallayen da ake bin kungiyar ta Aljeriya.Rabon JSe Kabylie ta lashe confederation cup tun shekara ta 2002. Yayin da Wannan dai shi ne karo na biyu cikin shekaru uku da Raja ke cin wannan kofi baya ga na shakara ta 2018. A jimlance dai, sau takwas kungiyar Casabalanca ta ci kofuna dabam-dabam na Afirka ciki har da kofin zakarun Afirka biyu. Ba safai ake samun kungiyoyi da suka taba nuna wannan bajinta a muhimman gasannin wannan nahiya sau da dama ba, in ban da su TP Mazembe ta Kwango, da ke cikin kungiyoyin da suka lashe kofin gasar zakarun Afirka na Champions Lig da na Kofin confederation sau da dama.

 

Novak Djokovic ya samu nasara a gasar ATP

Wimbledon Championships 2021 | Finale Novak Djokovic vs. Matteo Berrettini
Hoto: Paul Childs/REUTERS

Novak Djokovic ya zama dan wasa na farko da ya samu nasarar kai wa ga wasan karshe na ATP bayan da ya samu nasara a kan Matteo Berrettini dan kasar Italiya da ci shida da bakwai da shida da hudu da kuma shida da uku abin da ya ba shi nasarar lashe kofin na Wimbledon karo na shida. Nasarar ta shi da ta ba shi damar samun tikitin zuwa gasar ATP da za a gudanar daga ranar 14 zuwa 21 ga watan Nuwambar wannan shekara. Da yake jawabi kan nasarar ta sa Djokovic ya nunar da cewa ya yi matukar farin ciki da ya samu tikitin zuwa gasar ATP da za a gudanar a Turin da wuri. Wannan dai shi ne karo na 14 da Djokovic ya samu nasarar zuwa wasan karshen na ATP. Mai shekaru 34 a duniya, wanda kuma ke kan hanyarsa ta fatan zama dan wasan Tennis da ke kan gaba da ya samu nasara karo na bakwai, ya lashe wasanni 34 cikin 37 da ya yi a wannan shekara.