1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a hukunta kungiyoyin da za su bar gasar zakarun Turai

Abdul-raheem Hassan MNA
April 26, 2021

Sabbin dokokin da suka samu amincewa da gagarumin rinjaye a majalisar koli na hukumar, ya tanadi hana kowace kungiya shiga gasar kwallon kafa ta cikin gida a Italiya.

https://p.dw.com/p/3sbbI
Großbritannien Schals der englischen Fußball-Premier-League-Teams
Hoto: Alastair Grant/AP Photo/picture alliance

Hukumar kwallon kafa ta kasar Italiya ta sabunta dokokin hukunta duk kungiyar da ke nuna sha'awar ballewa daga gasar zakarun nahiyar Turai zuwa sabuwar gasar da wasu kungiyoyi ke shirin girkawa ta European Super League.

Kungiyoyin Juventus da AC Milan da ke cikin gasar Serie A, na cikin kungiyoyin da ke shirin ballewa a Italiya zuwa sabuwar gasar European Super League.

Sauran kungiyoyin sun hada da wasu manyan kungiyoyin da ke a Ingila kamar Arsenal da Chelsea da Liverpool da Manchester City da Manchester United da kuma Tottenham, sai Atletico Madrid da Bercelona da Real Madrid a kasar Spain.