Jama'a na yin ƙaura daga Somaliya
December 26, 2011Majalisar .Ɗinkin Duniya ta ba da sanarwa cewa mutane a ƙalla dubu 300 ne yan ƙasar Somaliya farin da ya hadasa yuwan ya tilasta wa arcewa zuwa gudun hijira a ƙasar Etiopiya da ke maƙobta da ƙasar
Sanarwa ta ce a kowacce rana ɗaruruwan jama'ar ne ke yin ƙaura daga ƙasar Somaliya a ya yin da faɗa da ake gwabzawa tsakanin ƙungiyar yan tawaye ta Al-Shebab da dakarun gwamnatin ke ƙara yin ƙamari. Wani jam'in Majalisar Ɗinkin Duniya da ke a sansani yan gudun hijira na Dolo Ado ya ce lamarin ya kazance saboda rashin wuraran da ba a da su na fake yan gudun hijira waɗanda ke tuɗaɗowa a kowacce rana. Ya kuma ce yan gudun hijira su kan sayar da abinci da ake ba su domin sayan tufafai ko wata cimakar ta daban irin su madara shinkafa da suga.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu