Jam'iyar CDU a wani hali na tsaka mai wuya
September 14, 2010Yanzu haka dai muhawara ta kara tsananta a tsakanin wakilan jam'iyar CDU a nan Jamus, game da alkiblar da jam'iyar zata sanya gaban ta. Muhawarar a wannan karo ta taso ne sakamakon sabani tsakanin jam'iyar ta CDU da shugaban kungiyar Jamusawan da aka koro su daga yankunan gabashin Turai, Erika Steinbach da kuma yadda jam'iyar zata duba batun zaman baki a Jamus. A wannan mako jam'iyar tayi zaman taron manyan shugabannin ta inda ta yi nazarin wannan al'amari.
Masu zanga-zanga yan kalilan ne suka hallara a hedikwatar jam'iyar ta CDU a Berlin, inda sukai ta daga kwalaye dake gargadin jam'iyar da kada ta kuskura ta kauce daga dabi'un Kirista da aka dora manufofi da wanzuwarta a kansu. Mafi yawan wadannan yan zanga-zanga matasa ne na jam'iyar da suka fito daga yankin Ruhr. Daya daga cikin su, shine Jacek Spendel, wanda kuma yake nunar da cewa:
"A yanzu haka babu wani abu mai yawa da ya rage tattare da manufofi na addinin Kirista da darajar da aka sani na wnanan addini da alkiblarda jam'iyar mu ta sanya a gaba a ya shafi wnanan addini. Game da haka, bana ganin wani banbanci tsakanin jam'iyar tamu ta CDU da jam'iyun SPD da FDP. Dukan su iri daya ne, al'amura kuwa ba zamu kyale su ci gaba haka ba.. Ko dai shugabannin namu dake can sama su farka, ko kuma mu fara tunanin yiwuwar kafa sabuwar jam'iya ta kashin kanmu".
Cikin jam'iyar ta CDU yanzu haka, akwai mutane masu yawa dake irin wnanan tunani. Ba kuma karon farko ba kenan da irin wannan tunani ya shiga zukatan jama'a, musmman tun lokacin da shugabar jam'iyar, Angela Merkel ta karkatar da ita zuwa ga ra'ayi na tsaka-tsaki, sai dai a wnanan karo, tunanin yiwuwar kafa sabuwar jam'iyar ya kara tsananta fiye dda da can. Sai dai ita kanta Merkel ta kare matakan da take dauka na neman cimma bukatun bangarori dabam dabam a al'amuran siyasa.
"Ina son kara karfafa cewar mu jam'iyar mu an dora ta ne kan manuifofi guda ukku: manufar matsakaicin ra'ayi da manufofi na addinin kirista da kuma ra'ayi na yan mazan jiya. Babu ko daya daga cikin wadannan mandfofi ukku da kuwa zamu yi watsi dashi, saboda dukkan su uku ne suka maida mu jam'iya ta jama'a. Ina kuma ganin cewar aikin jam'iyar CDU ne ta ga cewar ba'a sami wata jam'iya da zata kasance da manufofi na ra'ayin rikau ba".
Wadannan matakai na shugaban gwamnati Merkel sun sanya jam'iyar ta CDU cikin wani mawuyacin hali. A hannu guda bata son yin watsi da manufofin da aka dora ta a kansu, inda tsoffi cikin jam'iyar suke bukatar ta ci gabada dogara ga tsari na Kirista da sune suka kafa ta, yadda idan zabe yazo, zasu ci gaba da nuna goyon bayan su gareta. To sai dai wannan ba abu ne mai sauki ba. Jam'iyar ta dakatar da al'adar aikin soja na bautawa kasa, ga kuma sabuwar muhawara game da zaman baki da bukatar sajewar su da rayuwa a Jamus, ga kuma sabani da Erika Steinbach, shugaban Jamusawan da aka koro su daga yankunan gabashin Turai, wadda sananiya ce cikin jam'iyar ta CDU.
Duka wadannan al'amura sun kai ga tambayar, shin za'a sami bullowar wata sabuwar jam'iya ce ta masu ra'ayin yan mazan jiya a Jamus, kamar misali irin yadda ya faru a Holand, inda Geert Wilders ya kafa jam'iyar sa ta masu ra'ayin rikau. Shin wa zai iya dakatar da wadanda suke ci gaba da nuna rashin gamsuwar su da jam'iyar ta CDU a yanzu. Masana suka ce ko da shike masu nuna rashin gamsuwar basu da wani kakaki mai mai karfi a yanzu, amma sun yi imanin nan gaba, shugaban jam'iyar a jihar Sachsen, Stanislaw Tillich zai iya cike wannan gibi.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Abdullahi Tanko Bala