Jam'iyyar CDU ta gudanar taro
July 19, 2010Gwamnatin gamin gambiza ta Angela Merkel da ke mulkin Jamus ta yi ƙoƙarin ba al'umar tabbacin cewa har ila yau tana da ƙarfin tafiyar da mulki duk da murabus na gwamnan jihar Hamburg da ke zaman irinsa na shida da ta fuskanta a wannan shekara. Bisa ga dukkan alamu gwamnatin tana fuskantar janyewar gaggan shugabanninta da suka haɗa da magajin garin na Hamburg mai cike da farin jini, wato Ole von Beust.
Murabus ɗin von Beust na zaman irinsa na shida da gwamnatin ta fuskanta tun daga watan Satumban bara. A wani taro da jam'iyyar CDU ta yi a yau Litinin 'yan siyasarta sun yi watsi da abin da ya faru tare da lasan takobin samar da sabbin ƙwararru. A dai halin yanzu matsayin yardar da al'uma suka bai wa Merkel yayi ƙasa zuwa kashi 35 daga cikin ɗari.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu