Jamus na nazari kan Film ɗin ɓatanci wa Islama
September 18, 2012A ƙasar Jamus yanzu haka ana muhawara kan film ɗin ɓatancin da aka yi wa addinin Musulunci, wanda wani ba'Amirke ya wallafa. Inda yanzu haka yan siyasa da sauran al'umma ke tofa albarkacin bakinsu kan ko faɗin albarkacin baki abune da ya kamata kada ya kai ga cin mutunci wani, abinda zai kai ga haddasa tarzuma.
Da yake faɗin albarkacin bakinsa kan lamarin shugaban majalisar dariƙar Katholika na Tarayyar Jamus Robert Zollitsch, yace wannan Filmɗin abune da ba za a lamunta da shi ba, kuma abun tsokalane na ba gaira ba dali. A ɓangaren jam'iyun siyasa na Tarayyar Jamus, babbar jam'iyar adawa ta SPD da kuma jam'iyar kare mahalli ta The Green suna masu ra'ayin cewa film ɗin abun haushi ne, amma baya ɗauke da abinda za iya cin tara bisa yayata shi. Ita kuwa ministar shari'a ta Tarayyar Jamus Leutheusser-Schnarrenberger, kawo yanzu bata abimnce da ɗaukar matakin shari'a ba, amma tana mai cewa ya kamata a ƙarfafawa al'umma gujewa kalaman tsokala. .To shin ko ya ya masana shari'a ke kallon batun hana nuna faifayin vedio na ɓatancin. Christoph Gus masanin kundin tsarin mulki ne dake jami'ar Bielafeld
"A zahiranci bisa doka kumomi basu da wani hurumi na cewar komai. Batun da ya shafi addini yana cikin kundin tsarin mulkin Jamus, amma bai fayyace wata matsaya ba, an barshi ne a buɗe, babu batun parpaganda ko ɓatanci da aka abbata a cikinsa"
Da yake amsa tambaya kan bisa matsayin gwamnatin Jamus a wannan film na ɓatanci wa addinin Islama, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle cewa ya yi.
"Wannan faifayin vedio abun kaito ne, ba shi da wani hurumi a garemu Jamusawa da ma matsayin demokradiyya da muke bin tsarinta a ƙasashen yamma. Mu ƙasace da ta yi ammana da ko wane addini. To amma fa wannan vedio ba hujja bace ta tada tarzuma"
To shin ko wane mataki gwamnatin Tarayyar Jamus ke son ɗauka bisa faifayin vedio da ake ci gaba da yaɗawa, ko za a iya haramta nuna shi a ƙasar ta Jamus? Westerwelle yace
"Wannan shine abinda muke dubawa, domin ba za mu yarda aci gaba da yaɗa wani abunda yake cin mutuncin wani ba, abinda muke so doniya ta sani kenan. Za mu bi doka don ganin cewa yancin faɗar albarkacin baki, bai muzantawa wani addini ba, kuma ana iya cin taran wanda ya aikata hakan, don haka abinda nake faɗa shine a mutunta yancin kowa, harda na musulmai"
To shin mi dokar ke cewa kan yancin faɗin albarkacin baki, gadai masanin shari'a Gus abinda yake cewa
"Yancin faɗin albarkacin baki, wani abune daban, ko wane yana da cin fadin albarkacin bakinsa, kowa na iya tsokaci kan wani abu. Amma fa dole mutun ya ɗau alhakin duk abinda ya furta abakinsa, wannan kuwa ya shafi har da addini"
Yanzu haka hukumomi da alƙalai dole su ci gaba da yin muhawara tsakanin yancin fadin albarkacin baki, da kuma yancin walalar addini da mutunta ko wane addini da ma gujewa abinda zai kai ga da tada tarzuma.
Mawallafa: Rachel Gessat/ Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi