1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na adawa da tallafin Bankin Turai

Gazali Abdou Tasawa
May 5, 2020

Kotun tsarin mulkin Jamus ta bukaci Babban Bankin Turai da ya gabatar da hujjojin da ke nuni da cewa shirinsa na tallafa wa tattalin arzikin wasu kasashen Turai bai saba wa doka ba.

https://p.dw.com/p/3boFD
Deutschland Verfassungsgericht Tornado Afghanistan
Hoto: AP

Kotun tsarin mulkin kasar Jamus ta bukaci Babban Bankin Turai da ya gabatar da hujjojin da ke nuni da cewa shirinta na bayar da bashi ga wasu kasashen Turai masu fama da matsalar tattalin arziki da nufin tallafa masu ga fita daga matsalar bai saba wa doka ba.

 Babban bankin kasar ta Jamus ya yi barazanar janyewa daga cikin shirin na tallafawa tattalin arzikin kasashen Turan idan har a cikin watanni uku masu zuwa Babban Bankin Turai bai gabatar masa da hujjojin da ke nuni da cewa shirin tallafin bai keta haddin dokokin Turai.

 Kotun tsarin mulkin kasar ta Jamus ta ce ba za ta yi biyayya ga matsayar da Kotun Kolin Turai ta dauka ba a shekara ta 2018 inda ta amince da shirin Babban Bankin Turan na tallafawa tattalin arzikin kasashen nahiyar, matakin da alkalan kotun kolin ta Jamus ta ce Babban Bankin turan ya dauka ba tare da la'akari da illar da hakan zai yi wa tattalin arziki ba.