Jamus na shirin karbar shugabancin Turai
June 29, 2020Batun annobar corona ta girgiza shirin gwamnatin tarayyar Jamus a shugabancinta na kungiyar tarayyar Turai musamman a dangantaka da Afirka kamar yadda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nunar a jawabinta kan manufofin Jamus a shugabancin kungiyar tarayyar Turai.
Ta ce tuni "An hango cewa kasashe da dama na Afirka za su fuskanci kalubale masu yawa na wannan annoba. A saboda haka dole ne mu hada kai baki daya mu samo masalaha da kuma hanyoyin da za mu rage radadin wannan abu. A lokaci guda kuma za mu iya koyon abubuwa da dama daga kasashen Afirka wadanda su ma suke da nasu hanyoyi na shawo kan wannan annoba."
Babu shakka, kungiyar tarayyar Turai na bukatar kulla sabon kawance da Afirka, yarjejeniyar da mai yiwuwa za a sanya wa hannu yayin taron koli tsakanin Afirka da Turai a watan Oktoba. To amma idan aka gaza cimma yarjejeniya kan cinikayya da kuma batun kudade to akwai yiwuwar sabon kawance a tsakanin bangarorin biyu ya kasance na fatar baka kawai ko da kuwa a karshe sun sanya hannu akan yarjejeniya a cewar Carlos Lopes wakilin kungiyar tarayyar Afirka a kungiyar EU.
Ya ce "Afirka da nahiyar turai suna da muradu na bai daya ta fuskar cinikayya da magance matsalar kaurar jama'a da zaman lafiya da tsaro. Saboda haka muna da manufofi na bai daya, to amma har kawo yanzu wannan tarihi da alkawura da dama da aka cimma a baya basu fidda mu daga tsari na mulkin mallaka ba, na samar da kayan sarrafawar masana'antu da ake fitar da su zuwa kasashen waje. Lokaci ya yi da za sauya wannan."
To sai dai a cewar Anke Kurat na kungiyar VENRO da ke nazari kan manufofin kasa da kasa yace akwai dama ta yin gyara.
Ya ce "Kasashen Afirka har yanzu sun dogara da tsammanin samun tallafi da gudunmawar kudi daga kungiyar tarayyar Turai. To amma tsarin samar da kudaden na cin tura musamman a tsakanin mambobin kasashen turai. Lamari kuma ya yi kamari da aukuwar annobar corona."
Afirka dai na cike da fata mai yawa cewa Jamus za ta taka muhimmiyar rawa ba don komai ba saboda Jamus saboda baya ga kasancewarta kasa mafi karfin tattalin a nahiyar turai ita ce kuma ta fi bada gudunmawa a kasafin kudin EU a saboda haka ta ke da karfin fada a ji tarayyar turai. To amma a cewar Obiageli Ezekwesili yar Naajeriya kuima kwararriya a fannin tattalin arziki ya kamata Jamus ta kara jajircewa a dangantakarta da Afirka.
Ta ce "Shugabancin kungiyar tarayyar turai na nufin cewa ya kamata Jamus ta tashi tsaye, ta daina fakewa. Lokaci ya yi da za ta kara azama wajen yin aiki tare da Afirka a bisa manufa ta fahimtar juna domin shata sabuwar hanyar da za ta magance abubuwan da basu dace ba"
Akwai dai kalubale a gaban Jamus wajen cimma dorewar danganka a tsakanin nahiyoyin biyu. Misali cinikayya da ake yiwa lakabni da yarjejeniyar Cotonou a tsakanin bangarorin biyu za ta kare a karshen wannan shekarar ta 2020 da kuma yarjejeniyar da ke tangal tangal tsakanin turai da tsoffin kasashen da nahiyar turai ta yiwa mulkin mallaka, yarjejeniyar da za ta kare a watan Maris amma aka tsawaita zuwa karshen wannan shekarar.