1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin ficewar sojojin ketare a kasar Mali

Binta Aliyu Zurmi
November 24, 2022

Bayan kwashe shekaru 10 na kokarin samar da zaman lafiya a kasar Mali, Jamus ta sanar da janye dakarunta daga cikin tawagar kiyaye zamna lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA da ke Mali a 2024.

https://p.dw.com/p/4K1ID
Sojojin Jamus a Mali
Sojojin Jamus a MaliHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Kungiyoyin fararen hula a Mali tare da al'ummar kasar da ta kwashe shekaru ta na fama da ayyukan ta'addanci na fargabar ficewar sojojin kasashen waje daga kasar zai zamo wani babban koma baya a bangaren tsaron kasar. A cewar Soulaymane Camara da ke zama shugaban wata kungiyar kare hakkin bil Adama, Mali ba ta da karfin sojin da za ta kawo karshen 'yan ta'adda a kasar ita kadai,

"Ficewar wadannan sojojin da ke taimaka wa sojojinmu yakar 'yan ta'adda, akwai damuwa a tatare da hakan. Za su bar gurbi a fannin tasron kasar nan wanda sojojinmu ba za su iya cike shi ba, dakarun rundunar MINUSMA na aikin sintiri a wuraren da ke da hadari, kuma ficewarsu dole sai Mali ta nemi yadda za ta mayar da gurbinsu"

Afghanistan | Soldaten in Westafrika
Hoto: Arne Immanuel Bänsch/dpa/picture alliance

To a yayin da al'ummar kasar Mali ke nuna damuwarsu a kan matakin da sojojin kasashen waje ke dauka na ficewa daga kasar, da alama jagororin soji da ke rikon kwarya a kasar ta Mali sun yi maraba da wannan mataki, inda da farko suke tunanin kamar Jamus ta bi sahun Faransa ne wadda ta kwashe dakarunta tun a wattan Augusta a cewar mataimakin shugaban gwamnatin rikon kwarya Fousseynou Ouattara a tattaunawar sa da tashar DW.

"Wannan matakin na Jamus akwai manufa a cikinta fiye da yadda muke tunani, mun dauka za su yi wa Faransa makauniyar biyaya. Jamus na daga cikin manyan kawayenmu da mu'amalarmu ke da matukar muhimmanci,  idan har Jamus ta fahimci bukatar mu ta kare kasarmu da kanmu ba tare da sojojin kasashen waje ba, ina ganin ya kamata Jamus ta bamu goyon baya"

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock  yayin ziyararta a Mali
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock yayin ziyararta a MaliHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Ana dai tunanin tun lokacin da Faransa ta kawo karshen dakarun Barkhane da na kasashen Turai na Takouba sannan Mali ta fice daga cikin kungiyar kasashen G5 Sahel, mahukuntan birnin Bamako suka kirkiri yanayin da dakarun kasashen ketare za su fice daga kasar. A nasa bangaren Amadou Maiga sakataren gwamnatin shi ma ya goyi bayan ficewar sojojin daga kasarsu.

"Dama mun jima muna jiran wannan lokacin, ba Jamus ce kadai za ta fice ba akwai sauran kasashe da zasu biyo baya. Muna matukar godiya da dakarun Berlin bisa gudumawarsu, lokaci ya yi da zamu karbi ragamar maido da zaman lafiyar kasarmu, muna cike da sanin ba abu ne da zai zo mana da sauki ba, amma dai za mu fuskance shi da taimakon wasu gyare-gyare da za mu yi kuma za mu yi nasara"

Yanzu dai mahukuntan na Mali na shirin daukar sabbin sojoji a wannan shekarar da yawansu ya kai mutum dubu 26 amma za a dauki lokaci wajen koyar da su dabarun yaki kafin a kai su fagen daga.