1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janar Diendere ya dage zaben Burkina Faso

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 18, 2015

Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Burkina Faso sun sanar da dage zabukan kasar da kuma sanya dokar takaita zirga-zirga a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/1GYNj
Burkina Faso Ouagadougou General Gilbert Diendere
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Bayan da wani hafsan soja da ke zaman babban aboki ga tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore ya dare kan karagar mulkin kasar ta hanyar juyin mulki da sojoji suka yi wa gwmnatin rikon kwaryar kasar ne, gwamnatin mulkin sojan ta sanar da dage zabukan da aka shirya yi cikin watan Oktoba mai zuwa tare da sanya dokar takaita zirga-zirga a kasar baki daya.

Kakakin rundunar sojojin Burkina Fason ya sanar da haka inda ya kara da cewa sun rusa gwamnatin rikon kwaryar da ke kasar kana an sanya dokar takaita zirga-zirga ta sa'oi 24 tare kuma da rufe dukkanin kan iyakokin kasar. Wannan dai shi ne karo na shida da sojoji ke juyin mulki a kasar tun bayan da ta samu 'yancin cin gashin kanta daga Faransa.