Janar Gilbert Diendere ya ki mika makamai
September 28, 2015Gwamnatin rikon kwarya ta Burkina Faso ta zargi madugun juyin mulkin da ya ci tura Janar Gilbert Diendere da yin garkuwa da sojojin da aka dorawa alhakin kwance wa rundunarsa damarar yaki. Cikin wata sanarwa da ta fitar, fadar mulki ta Wagadugu ta ce Diendere ya ki mika kai ga bukatar mika makamai, yana mai cewa gwamnatin rikon kwarya ba ta da hurumin rusa rundunar da ke tsaron fadar shugaban kasa da kuma karbe makamai daga hannun dakarunta.
A cewar gwamnati dai, Janar Diendere ya yi garkuwa da sojojin gwamnati da kuma dogaran rudunarsa da suka nuna alamun yin biyayya ga umurnin gwamnati. Dama dai rundunar sojojin Burkina Faso ta ce tana fuskantar turjiya wajen raba Janar Diendere da kuma sojojin da ke yi masa biyayya da makamai.
Idan za a iya tunawa dai gwamnatin rikin kwarya ta rusa rundunar da ke tsaron fadar shugaban kasa bayan da shugabanta wanda kuma na hannu dama ga Blaise Compaore ya aiwatar da juyin mulkin da bai samu karbuwa ba.
Tuni dai Faransa da ta yi wa Burkina Faso mulkin mallaka ta rufe makarantunta a birnin Wagadugu tare da kira ga 'yan kasarta da takaita zirga-zirga sakamakon yiwuwar barkewar tashin hankali.